Birtaniya

Birtaniya ta boye laifukan yakin da sojojinta suka aikata - Rahoto

Sojojin Birtaniya a lardin Helmand dake Afghanistan.
Sojojin Birtaniya a lardin Helmand dake Afghanistan. REUTERS/Ahmad Masood

Wani bincike ya nuna cewar, gwamnatin Birtaniya da rundunar sojin kasar sun boye bayanai masu tasiri dake nuna yadda sojojin kasar suka dinga aikata laifuffukan yaki wajen cin zarafin fararen hula a kasashen Afghanistan da Iraqi.

Talla

Wasu bayanan gwamnati guda biyu da aka tsegunta daga binciken da aka yi, ya bankado yadda sojin Birtaniya suka kashe fararen hula cikin su harda yara kanana da kuma azabtar da mutane a kasashen na Iraqi da Afghanistan.

Jami’an sojin da suka gudanar da bincike kan lamarin sun gano shaidun aikata laifuffukan yaki, wanda suka zargi kwamandodin sojin da boyewa saboda dalilan siyasa.

Kafofin yada labaran Birtaniya da suka gudanar da binciken sun ce ma’aikatar tsaron Birtaniya bata da niyyar hukunta duk wani soja da aka samu da laifi, yayin da ta musanta zargin.

Jaridar Sunday Times tace masu binciken sojin sun gano zarge zarge kan yadda aka rubuta rahotanni karya domin hana tuhumar manyan jami’an sojin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.