Ana tunawa da wadanda harin ta'addanci ya shafa a Faransa

Dakarun yaki da ta'addanci a Faransa
Dakarun yaki da ta'addanci a Faransa REUTERS/Charles Platiau

Birnin Nice na kasar Faransa wanda ta fuskanci harin ta’addanci mafi muni a nahiyar Turai, na karbar bakwancin taron kasa- da – kasa don nazari kan halin da wadanda harin ta’addanci ya rutsa da su ke ciki.

Talla

An zabi birnin Nice na kasar Faransa ne domin karbar bakuncin babban taron na kasa-da-kasa karo na 8 na wadanda ta'addanci ya shafa, kasancewar daya daga cikin biranen duniya daga suka fuskancin muggan hare-haren ta’addanci.

A narar 14 ga watan Yulin shekarar 2016, birnin Nice ya gamu da harin ta’addanci mafi muni, wanda ya hallaka mutane 86, da jikkata wasu dama.

Toron zai yi Nazari kan halin da iyalai ko wadanda hare-hare ya rutsa da su ke ciki, da kuma hanyar inganta kulawa da su.

Guillaume Denoix de Saint Marc, Darektan kungiyar dake sa ido kan muatanen da ta’addanci ya ritsa da su a Faransa, da ke shirya wannan taro na birnin Nice, na ganin matakin a matsayin wata sabuwar fasaha na baiwa mutanen da hare-haren ta’addanci ya shafa a Duniya samun mafuta daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.