Faransa

Mata 116 ne abokan zaman su suka kashe su a Faransa a 2019

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron REUTERS/Philippe Wojazer

Dubun dubatan mutane ne suka fito tattaki a birnin Paris don neman kawo karshen cin zarafi mai nasaba da jinsi a kasar da akalla mata 116 ne abokan zamansu na da, da na yanzu suka kashe a wannan shekarar, abin da ya kawo tada jijiyar wuya a kasar.

Talla

Da dama daga cikin masu tattakin sun a dauke da kwalayen da aka makala hotunan ‘yan uwa ko abokansu da aka kashe ta wurin irin wannan nau’ in cin zarafi.

Akasarin masu zanga – zangar mata ne, kuma kusan kungiyoyi da jami’iyyun siyasa da kungiyoyin kwadago 70 ne suka shirya wannan tattaki a daukacin kasar Faransa.

Wata kungiya mairajin kare hakkin mata ta ce matan da abokan zaman su suka kashe a wannan shekarar sun kai 137.

Ta ce duk bayan kwana uku ana kashe mace daya a Faransa,kuma mazn su, ko abokan zaman su maza, na da, da na yanzu ne ke aikata wannan aika – aika, yayin da matan Faransawa dubu 220,000 ne ke fuskanta cin zarafi a zaman auren su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI