Birtaniya

Wani mahari da wuka ya illata mutane a Landan

Firaministan Birtaniya Boris Johnson.
Firaministan Birtaniya Boris Johnson. Parliament TV via REUTERS

Mutane da dama ne suka samu raunuka a wani harin da mahukuntan kasar suka bayyana cewa na ta’addanci ne a birnin London. Tuni dai aka bindige maharin har lahira.

Talla

Maharin wanda ke dauke da zungureriyar wuka a kusa da wata babbar gada da ke tsakiyar birnin London, wadda a shekara ta 2017 ma aka murkushe wani yunkurin harin ta’addanci a cewa jami’an tsaro.

Neil Basu, shugaban sashen yaki da ayyukan ta’addanci a Birtaniya, ya ce tuni aka bindige maharin lokacin da ake yunkurin murkushe shi, kuma farmakin nasa ko shakka babu na ta’addanci ne.

Wasu majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa maharin na dauke da wasu abubuwa masu fashewa a jikinsa, kuma yayin da jami’an tsaro suka killace unguwar da lamarin ya faru don ci gaba da bincike.

Wasu hotuna da aka yada a kafafen sada zumunta, sun nuna wanu mutum kwance a kasa amma da wuka rike a hannunsa, yayin da ‘yan sanda dauke da bindigogi ke tsaye a kansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI