Isa ga babban shafi
Faransa-Mali

Ba harin ta'addanci ne ya kakkabo jiragenmu a Mali ba- Faransa

Shugaban Kasar Faransa Emmanuel Macron.
Shugaban Kasar Faransa Emmanuel Macron. Bertrand Guay/Pool via REUTERS
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu
Minti 1

Ma’aikatar tsaron Faransa ta fitar da sanarwar da ke nesanta hadarin jiragen yakinta biyu a Mali da ya hallaka sojin kasar 13 da farmakin mayakan jihadi.

Talla

Sanarwar ta Faransa na matsayin martani kan ikirarin kungiyar mayakan jihadi ta yammacin Afrika ISWAP da ta bayyana cewa jiragen biyu sun yi karo da juna ne bayan harbin dayansu da mayakan sukayi.

Sai dai sanarwar ta Faransa ta ruwaito babban Hafson sojin kasar Francois Lecointre na cewa babu wata hujja da ke nuna mayakan na ISWAP ne suka kakkabo jiragen biyu, maimakon haka bincikensu ya nuna cewa jiragen biyu sun yi karo da juna ne wanda ya haddasa hadarin, dai dai lokacin da suke laluben maboyar mayakan ta’addan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.