London

Maharin London tsohon dan ta'adda ne- 'Yan sanda

Yankin da aka kaddamar da farmakin na wuka a birnin London
Yankin da aka kaddamar da farmakin na wuka a birnin London Reuters/Peter Nicholls

Rundunar ‘yan sandan birnin London ta tabbatar da cewa maharin da ya hallaka mutane 2 da wuka cikin daren jiya Juma’a tsohon dan ta’adda ne da aka saki daga gidan yari bara.

Talla

Maharin wanda aka yi zargin ya na sanye da rigar bom tuni jami’an ‘yan sanda suka harbe shi har lahira yayinda aka garzaya da mutane 3 da suka jikkata a harin asibiti.

‘yansanda dai sun bayyana maharin dan shekaru 28 da suna Usman Khan kuma ya aikata laifuka a kasar da suka kai shi gaz aman yari wanda kuma ya kaddamar da farmakin shekara guda bayan fitowarsa.

Neil Basu, shugaban sashen yaki da ayyukan ta’addanci a Birtaniya, ya ce tuni aka bindige maharin lokacin da ake yunkurin murkushe shi, kuma farmakin nasa ko shakka babu na ta’addanci ne.

Wasu hotuna da aka yada a kafafen sada zumunta, sun nuna wani mutum kwance a kasa amma da wuka rike a hannunsa, yayin da ‘yan sanda dauke da bindigogi ke tsaye a kansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI