Birtaniya-Ta'addanci

Birtaniya na nazarin dokar sakin fursunonin 'yan ta'adda daga Yari

Firaministan Birtaniya Boris Johnson.
Firaministan Birtaniya Boris Johnson. Parliament TV via REUTERS

Ma’aikatar shari’a a Birtaniya ta shigar da wani kudirin gaggawa da ke bukatar bitar tsarin sakin mutanen da ake zargi da laifukan ta’addanci daga gidan yari, kudirin da ke zuwa bayan harin shekaran jiya juma’a da ya hallaka mutane 2.

Talla

Firaministan Birtaniyan Boris Johnson ya bayyana cewa sakin maharin cikin gaggawa daa yari ne ya haddasa harin na ranar juma’a inda ake saran a jawabin da zai gabatar yau Lahadi ya caccaki tsarin na sakin Fursunoni masu tabon ta’addanci daga yari tun kafin kammaluwar wa’adinsu.

Matashin maharin wanda aka bayyyana sunansa da Usman Khan mai shekaru 28 ya kammala rabin wa’adin da aka dibar masa ne a yari, inda aka fito dashi don lakantar ilimin doka tare da gyara halayensa a tsawon sauran rabin wa’adin daya rage masa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.