Gwamnatin Faransa na kokarin magance rikicin ma'aikatan kasar
Wallafawa ranar:
Manyan jami’an gwamnatin Faransa sun yi ganawar gaggawa a jiya lahadi don kasance a cikin shirin ko-ta-kwana, yayin da kasar ke shirin fadawa yajin aikin gama gari a ranar alhamis mai zuwa domin nuna rashin amincewa da sabuwar dokar yin ritaya.
Ana hasashen cewa yajin aikin zai yi matukar shafar lamurran yau da kullum a sassan kasar ta Faransa, yayin da shugaban Emmanuel Macron ke ci gaba da kare matakin aiwatar da sauye-sauye ga tsarin zuwa ritaye a kasar.
Firaministan kasar Edouard Philippe da kan sa ne ya jagoranci zaman taron Ministocin na jiya lahadi a Paris.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu