Faransa

Jami’an agaji uku ne sun rasa rayukansu a Faransa

Jami’an agaji uku ne sun rasa rayukansu, lokacin da jirgi mai saukar angulu da ke aikin ceton wadanda ambaliya ta shafa ya yi hatsari kusa da birnin Marseille da ke kudancin Faransa a jiya lahadi.

Wani yanki da aka fuskanci ambaliya
Wani yanki da aka fuskanci ambaliya © RFI/Sonia Rolley
Talla

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana ahinin sa tareda girmama jami’an da suka rasa rayukan su.Ga baki daya mutane biyar ne aka sanar da mutuwar su a yankin.

Kama daga farkon watan Nuwamba,wasu yankunan Turai sun fuskanci ambaliya,lamarin da ya haifar da tsaiko ta fuskar zirga-zirga  musamman a Faransa.

Ministan cikin gidan Faransa Christophe Castaner, ya sanar da kaddamar da bincike domin gano dalilan faruwar wannan hatsari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI