Faransa

Zazzafar zanga-zangar Faransa ta kassara bangaren sufuri da Ilimi

Dubunnan al'ummar Faransa da ke ci gaba da zanga-zanga a rana ta biyu da fara bore kan sabuwar dokar ritaya.
Dubunnan al'ummar Faransa da ke ci gaba da zanga-zanga a rana ta biyu da fara bore kan sabuwar dokar ritaya. REUTERS/Gonzalo Fuentes

Yau Juma’a aka shiga rana ta biyu da fara zanga-zanga mafi girma a Faransa, zanga-zangar da kungiyoyin kwadago suka sha alwashin ci gaba da gudanarwa har zuwa lokacin da shugaba Emmanuel Macron zai janye kudurin gyara a dokar ritaya.

Talla

Yanzu haka dai kashi 90 na zirga-zirgar jiragen kasa aka dakatar yayinda aka dakatar da sufurun jirage masu tsananin gudu da ke amfani da lantarki dungurugum haka zalika an dakatar da galibin sufurun jiragen sama na kamfanonin Air France da EasyJet da kuma Ryanair.

Akalla manyan tashoshin jirage 16 a biranen kasar 9 aka kulle baya g ahana sufurin manyan motoci matakin da ya haddasa cinkoso da kuma karancin ababen hawa musamman a birnin Paris.

A bangare guda dubun dubatar ma’aikata sun kauracewa fita aiki inda makarantu suka ci gaba da kasancewa a rufe.

Adadin da suka sake fita zanga-zangar yau sun kai mutum dubu dari takwas yayinda kungiyar kwadago ke ikirarin cewa adadin ya haura mutum miliyan 1 da rabi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI