Amurka-Taliban

Amurka za ta koma teburin tattaunawa da Taliban

Shugaban Amurka Donald Trump.
Shugaban Amurka Donald Trump. Zach Gibson / GETTY IMAGES NORTH AMERICA / AFP

A yau Asabar Amurka da kungiyar Taliban za su dawo kan teburin tattaunawa a birnin Doha na Qatar, watanni uku bayan shugaba Donald Trump kwatsam, ya dakatar da kokarin da ake na lalubo mafita da ka iya kawo karshen yaki mafi tsawo da Amurka ta tsunduma ciki, kamar yadda wata majiyar gwamnatin Amurka ta bayyana.

Talla

A watan Satumba Amurka da kungiyar Taliban suna daf da sanya hannu kan wata yarjejniyar da kila wa kala ta kasancewar silar janyewar dubban dakarun Amurka a Afghanistan, amma hakan bai samu ba.

Har ila yau an sa ran cewa tattaunawar za ta share fagen ganawa tsakanin Taliban da hukumomi a Afghanistan, abin da zai kai ga yarjejeniyar kawo karshen yakin da aka shafe sama da shekaru 18 ana gwabzawa a kasar.

Amma a cikin watan ne shugaba Trump ya dakile wannan tattaunawar, ya kuma janye gayyatar da aka baiwa ‘yan Taliban

A wata ziyarar bazata da ya kai Afghanistan a makon jiya, Trump ya ce Taliban na neman kulla yarjejeniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.