Faransa

Ma'aikatan Faransa sun ci gaba da yajin aiki kan dokar Fansho

A yau Talata bangaren sufurin kasa da na sama ya gurgunce a Faransa sakamakon yajin aikin da ma’aikata ke yi don nuna adawa da shirin aiwatar da gyara a dokar ritaya da kuma biyan kudin fansho da gwamnatin Emmanuel Macron ke son aiwatarwa.

Dandazo ma'aikata da ke ci gaba da yajin aiki hade da zanga-zanga a Faransa.
Dandazo ma'aikata da ke ci gaba da yajin aiki hade da zanga-zanga a Faransa. REUTERS/Benoit Tessier
Talla

A cikin makon jiya an gudanar da irin wannan yajin aiki da ya yi matukar shafar lamurran yau da kullum saboda rashin ababan hawa a cikin manyan birane, yayin da aka samu barkewar tarzoma a wasu biranen kasar.

Tun fara wannan yajin aiki dai ba a ji ta bakin shugaba Macron ba, to sai dai Firaministansa Philippe da ke matsayin mai shiga tsakanin gwamnati da kungiyoyin kwadago, ya ce a shirye suke su shiga tattaunawa amma zuwa yanzu bai bayyana irin sassaucin da gwamanti za ta yi ba.

A gobe laraba ne firaministan zai fayyace gundarin shirin da kuma lokacin da zai fara aiki, tsarin da ma’aikatan ke adawa da shi, to sai dai kafin fayyace shirin, a yau litinin Edouard Philippe zai gana da wakilan sauran jam’iyyun siyasa da ke mara wa gwamnatin Emmanuel Macron baya.

Tuni dai sakataren kungiyar kwadagon kasar CGT Philippe Martinez ya yi gargadin cewa ma’aikata za su ci gaba da yajin aiki da shirya tarukan gangami har sai zuwa lokacin da gwamnatin ta jingine shirin baki daya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI