Turai

Gwamnatin Faransa ta fitar da wasu sharuda ga ma'aikatan kasar

Firaministan Faransa Edouard Philippe a yau laraba ya yi da yake gabatar da jawabin sa na kwantar da hunkula biyo bayan zanga-zanga daga kungiyoyin kwadagon Faransa,Edouard Philippe ya fayyace gundarin shirin gwamnatin kasar zuwa ma’aikatan Faransa.

Edouard Philippe Firaministan Faransa
Edouard Philippe Firaministan Faransa Thomas SAMSON / POOL / AFP
Talla

A jawabin da ya gabatar ga yan kasar, Firaministan Faransa Edouard Philippe yace, shekarun ritaya ga ma’aikatan kwadagon kasar zai ci gaba da kasancewa shekaru 62 ne.

Wanda hakan ke nufin karin shekaru biyu kafin soma amfana da kudin fansho.

Mista Philippe ya ce wannan batu na da saukin fahimta, Firaministan Faransa ya bayyana damuwar hukumomin kasar dangane da koken kungiyoyin kwadago na Faransa dake bukatar samun sassauci da fahimta daga shugaban kasar Emmanuel Macron da gwamnatin sa.

Firaministan Faransa Edouard Philippe ya duba shakku da Faransawa keda shi kan sabon kudirin, babu wani abun boye-boye a ciki a cewar sa.

Gwamnati a cewar Firaministan kasar ta Faransa,kungiyoyin kwadagon Faransa zasu cin moriyar wannan shiri nan gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI