Johnson da Corbyn na ci gaba da fafatawa a zaben Birtaniya
Wallafawa ranar:
Dubban al'ummar Birtaniya na ci gaba da kada kuri’a a zaben da zai fayyace makomar alakar kasar da EU, wanda ake saran ya kawo karshen rarrabuwar kan da batun ficewar kasar daga kungiyar tarayyar turai EU ya haifar.
Nasarar Firaminista Boris Johnson a wannan zabe dai ba shakka, a watan gobe zai kawo karshen kasancewar kasar cikin kungiyar kasashen Turai tsawon shekaru 46, gami da bude sabon babin tattalin arzikin kasar, gami da kulla alakar kusa da kasashen Amurka da China.
Sai dai nasarar jami’iyyar adawa ta Labour karkashin jagorancin Jeremy Corbyn, na nufin samun damar soke shirin Brexit na ficewar Birtaniya daga kungiyar kasashen Turai.
Gabannin zaben na yau dai, sakamakon wata kuri’ar jin ra’ayi, ya yi hasashen cewa Jam’iyyar Conservative mai mulki za ta yi nasara, amma da karamin rinjayen da zai tilasta mata kafa gwamnatin hadin gwiwa da ‘yan adawa.
Rumfunan zabe dubu 40 ne za su ci gaba da kasancewa a bude har zuwa karfe 10 na daren yau a kasar ta Birtaniya, wanda karo na uku kenan a kasar da zaben gama gari ke gudana cikin shekaru 4.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu