Birtaniya

Johnson ya sha alwashin fitar da Birtaniya daga EU bayan nasara a zabe

Firaministan Birtaniya Boris Johnson bayan nasararsa ta lashe zaben kasar na ranar Alhamis.
Firaministan Birtaniya Boris Johnson bayan nasararsa ta lashe zaben kasar na ranar Alhamis. REUTERS/Dylan Martinez

Bayan samun gagarumar nasara a zaben Birtaniya da ya gudana a jiya alhamis, Firaminista Boris Johnson, ya sha alwashin tabbatar da ganin ya kammala fitar da kasar daga EU wanda ya ce shi ne babban aikin da ke gabansa a yanzu haka.

Talla

Firaminista Boris Jonson wanda ya tsaya karkashin Jam'iyyar Conservative ya doka babban abokin adawarsa na Jam'iyyar Labour Jeremy Corbyn da kasa, inda ya samu kujeru 365 cikin kujeru 650.

Jam'iyyar ta Labour dai ta samu kuri'u 203 ne matakin da ya sanya Jeremy Corbyn shan alwashin kin sake tsayawa jam'iyyar takara a duk wani babban zabe da ke tafe.

Sauran jam'iyyun da suka tsaya takara a zaben sun hadar da SNP da ta samu kujeru 48 kana Liberal Democrats da kujeru 11 sannan DUP da kujeru 8.

Cikin jawabin Johnson bayan nasara a zaben, ya bayyana cewa ya zama wajibi Birtaniya ta kammala ficewa daga EU nan da ranar 31 ga watan Janairu, inda ya ke cewa nasarar tasa za ta zama izina ga majalisar kasar wajen mara masa baya tare da fitar da kasar daga Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI