Faransa

Harkokin sufuri sun durkushe a Faransa

Rikici tsakanin gwamnatin Faransa da kungiyoyin kwadagon da ke adawa da sauye-sauyen dokar fansho, ya tsananta a karshen mako bayanda aka shiga rana ta 11 na durkushewar harakokin sufuri a Faransa.

Jiragen kasa sun tsaya cik a duk kasar Faransa sanadiyyar yajin aiki
Jiragen kasa sun tsaya cik a duk kasar Faransa sanadiyyar yajin aiki REUTERS/Eric Gaillard
Talla

Firaministan Faransa, Edouard Philippe ya gargadi cewa, kasar ba za ta lamunta da durkushewar harakokin sufuri ba musamman a wannan lokaci da ake shirin gudanar da bikin Kirismati.

Durkushewar sufuri ta tsananta a jiya Lahadi, inda a birnin Paris bangaren zirga-zirgar ababan hawa kusan ya tsaya cik.

A makon jiya ne, Firaministan ya kaddamar da sauye-sauye a dokar fanshon kasar, wadda za ta bayar da damar dunkule wasu tsare-tsare 42 wuri guda, abin da zai tilasta wa mutane aiki na tsawon lokaci kafin ritaya.

Firaministan dai ya harzuka kungiyoyin kwadagon saboda bukatarsa ta rage kudaden fanshon ma’aikatan da suka yi ritaya bayan sun cika shekaru 62.

Yanzu haka kungiyoyjn kwadagon sun sanar da aniyarsu ta gudanar da gagarumar zanga-zanga a gobe Talata, inda ake sa ran dubban jama’a su fantsama kan tituna.

Masu shirya yajin aikin kasar na fatan maimata abin da ya faru a shekarar 1995, lokacin da suka tilasta wa gwamnati mai tsaka-tsakin ra’ayi janye shirinta na sauye-sauyen dokar fansho bayan jiragen kasa sun shafe tsawon makwanni uku cikin yajin aiki ana gab da gudanar da bikin Kirismati.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI