Faransa

Shugaban sabon shirin biyan kudaden fansho yayi murabus

Yayinda aka shiga rana ta 12 da soma yajin aikin gama gari a Faransa, musamman bangaren sufuri, babban jami’in gwamnatin kasar dake jagorantar shirin sauya tsarin biyan kudaden fansho yayi murabus, dalilin laifukan kin bayyana kadarori, da kuma karin mukamai da yake rike da su.

Jean-Paul Delevoye, babban jami’in gwamnatin Faransa dake jagorantar shirin sabon tsarin biyan kudaden fansho da yayi murabus.
Jean-Paul Delevoye, babban jami’in gwamnatin Faransa dake jagorantar shirin sabon tsarin biyan kudaden fansho da yayi murabus. AFP/Eric Feferberg
Talla

A karshen makon da ya kare Jean-Paul Delevoye ya soma shan tofin ala-tsine daga kungiyoyin Kwadago a Faransa, bayan da ya amsa laifin kin bayyana wasu mukamai har kashi 13 da yake rike da su a lokaci guda, baya ga shugabantar shirin sauya tsarin biyan kudaden fanshon kasar.

Daga cikin karin mukaman 13 da Delevoye ke rike da su akwai shugabancin wata gidauniyar ilimi, inda yake karbar albashin kusan euro dubu 5 da 400 a wata, kari kan albashinsa na gwamnati, abindaya sabawa dokar bayyana kadarorin masu rike da mukaman siyasa a Faransa ta 2013.

Tuni dai babban jami’in ya ce zai maidawa gwamnati jimillar haramtattun kudaden da ya karba a matsayin albashi da adadinsu ya zarta euro dubu 120.

A bangaren yajin aiki, gami da zanga-zangar adawa da sabuwar dokar biyan kudin fansho a Faransa kuwa, bangaren sufuri musamman na jiragen kasa ya ci gaba da kasancewa a gurgunce, inda yau litinin a birnin Paris da kewaye cinkoson ababen hawa ya kai tsawon kilo mita 630, sakamakon datse hanyoyin da masu zanga-zangar suka yi da safe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI