Amurka

Majalisar wakilan Amurka ta tsige Trump

shugaban Amurka Donald Trump.
shugaban Amurka Donald Trump. 路透社

Majalisar wakilan Amurka ta kada kuri’ar tsige shugaba Donald Trump daga mukamin sa saboda samun sa da laifin saba ka’idar aiki da kuma hana ta gudanar da aikin ta.

Talla

Yan Majalisu 230 suka amince da shirin tsige shugaban, yayin da 197 suka ki.

‘Yan jam’iyyar Democrats a majalisar wakilan sun ce ba su da wani zabi illa daukan wannan mataki na tilasta wa shugaba Trump fuskantar wadannan zarge zarge a majalisar dattawar kasar.

Trump zai fuskanci wadannan tuhume – tuhume a gaban majalisar dattawar kasar, inda ‘yan jam’iyyarsa ta Republican ne suka fi rinjaye, kuma ake sa ran za su wanke shi daga zargi.

Wannan kuri’ar da majalisar wakilan ta kada na zuwa ne watanni 4 bayan wani mai tonon silili ya yi korafi kan matsin lambar da shugaba Donald Trump ya yi wa shugaban Ukraine Volodomyr Zelensky kan sai kasar ta binciki abokin hamayyarsa dan Democrats, Joe Biden.

Shugaba Trump wanda shine shugaban Amurka na 45, na daga cikin shugabanni 3 a tarihin Amurka da ya fuskanci irin wannan yanayi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.