Wasanni-Kwallon kafa

Mutane da dama sun ji rauni yayin El Classico

Pro-independence protestors sit outside stock exchange during a demonstration marking the first anniversary of Catalonia's banned independence referendum in Barcelona
Pro-independence protestors sit outside stock exchange during a demonstration marking the first anniversary of Catalonia's banned independence referendum in Barcelona Reuters

A daidai lokacin da Barcelona da Real Madrid ke barje gumi a wasan hamayya da aka wa lakabi da El Clasico na farko a wannan kaka a daren Laraba, masu zanga – zanga da suka rufe fuskokinsu sun cinna wa kwandunan shara wuta, sannan suka yi ta jifan ‘yan sanda da duwatsu da kwalabe, yayin da ‘yan sanda suka yi ta mayar da martani da harsashin roba a wata unguwa kusa da filin wasan Barcelona na Camp Nou, inda wasan ke gudana.

Talla

Hukumar bada agajin gaggawa a yankin ta ce mutane 46 ne suka ji rauni a arangamar, ciki har da 8 da sai da aka garzaya da su asibiti don basu kulawa.

‘Yan sanda yankin Catalonia sun ce an kama mutane 9, kuma suna fuskantar tuhumar cin zarafin hukuma, tare da haddasa tashin hankali a cikin al’umma.

Masu zanga – zangar wadanda da dama daga cikinsu ke dauke da tutocin ‘yan awaren Catalan sun fara sanya shingaye a tsakiyar tituna kafin isowar ‘yan sanda a motoci da dama.

Sai da hankula suka kwanta a unguwar kafin masu kallon wasa suka fara barin filin wasan bayan an tashi karawar canjaras, babu ci.

Wannan ne rikici na farko a Catalonia tun watan Oktoba da kotun koli a Spain ta yanke wa shugabannin ‘yan awaren Catalan hukunci zama gidan yari sakamakon hannu da suke da shi a kokarin neman cin gashin kai ko ta halin kaka da bai yi nasara ba a shekarar 2017, lamarin da ya janyo mummunar zanga – zanga da fito – na – fito da ‘yan sanda.

Tun da farko sai da aka dage wannan wasa da aka shirya yi a watan Oktoba saboda zanga – zangar da ta barke a yankin.

‘Yan sanda sun ce masu zanga – zangar da suka kai 5,000 sun fara taruwa ne a wajen filin wasan sa’o’i 4 gabanin wasan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.