Faransa

Kotu ta daure tsohon shugaban Orange saboda takurawa ma'aikata

Didier Lombard, tsohon shugaban kamfanin sadarwar Faransa.
Didier Lombard, tsohon shugaban kamfanin sadarwar Faransa. REUTERS/Charles Platiau

Wata kotun Faransa ta aike da tsohon shugaban kamfanin sadarwar kasar Didier Lombard gidan yari na shekara guda bayan samunsa da laifukan muzgunawa ma’aikata, da ya tilastawa wasunsu daukar matakin kashe kansu a shekarun baya.

Talla

Hukuncin kotun da ke zuwa yau juma’a bayan zaman sauraron shari’ar biyo bayan zarge-zargen da ke nuna cewa akalla ma’aikata 35 ne suka dauki matakin kashe kansu tsakanin shekarar 2008 zuwa 2009 sakamakon takurar da Didier Lombard shugaban kamfanin na wancan lokaci ke musu.

Zaman shari’ar karkashin alkaliya Cecile Louis-Loyant wanda shi ne irinsa na farko tun bayan fasuwar zargin kan Lombard shaidu sun bayyanawa kotu matakan tsaurarawar da tsohon shugaban ya rika dauka a wancan lokaci ciki har da barazanar kora daga aiki.

Ka zalika wata hujja ta daban ta nuna yadda Lombard ya kori ma’aikata dubu 22 daga kamfanin cikin shekaru 3 kadai wanda ke nuna cewa daga shekarar farko ta kama aikinsa, Lombard sai da kori duk ma’aikaci 1 cikin 5 daya tarar a kamfanin sadarwar na Faransa da yanzuya sauya suna zuwa Orange.

Baya ga hukuncin kotun na aike Didier Lombard gidan yari na tsawon shekara guda dakuma dakatarwar aiki ta watanni 8 shi da mataimakinsa Louis-Pierre Wenes dukkanninsu za su biya tarar yuro dubu 15 yayinda kamfanin na Orange zai biya tarar yuro dubu 75.

Duk dai karkashin hukunci na mai shari’a Cecile Louis-Loyant karin wasu manyan jami’ai a kamfanin na Orange za su fuskanci dakatarwar aiki ta watanni 4 tare da biyan tarar yuro dubu 5.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI