'Yan cirani 7 sun mutu a kokarin tsallakawa Turai ta Turkiya
Akalla ‘yan cirani 7 daga kasashen Pakistan Bangladesh da kuma Afghanistan aka tabbatar da mutuwarsu yau Alhamis bayan nutsuwar kwale-kwalen da ke dauke da su a kokarinsu na tsallakawa nahiyar turai ta gabar tekun Van da ke gabashin Turkiya.
Wallafawa ranar:
Tekun dai na gab da kan iyakar Iran ne, hanya mafi sauki ga ‘yan ciranin wajen tsallakowa Turkiya da nufin shiga nahiyar Turai don samun rayuwa mai inganci.
Rahotanni sun bayyana cewa kwale-kwalen na dauke da fasinja fiye da 80 ne inda yanzu haka aka yi nasarar ceto mutane 64 wadanda ke karbar kulawar gaggawa a asibiti.
A cewar masu aikin ceto kwale-kwalen ya nutse ne da misalin karfe 3 na tsakaddare a dai dai yankin Bitlis da ke gab da Adilcevaz na Turkiya, inda nan take mutane 5 suka mutu yayinda wasu 7 kuma suka mutu a Asibiti.
Turkiya dai na matsayin hanyar shiga Turai mafi sauki musamman ga ‘yan ciranin da suka fito daga Nahiyar Asia, inda a cikin shekarar nan kadai ta sanar da kame ‘yan ciranin dubu dari 4 da 41 da dari 5 da 32.
Ko cikin watan jiya sai da Turkiyan ta yiwa takwarorinta kasashen Turai gargadin daina kame ‘yan ciranin masu kokarin tsallakawa kasashen.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu