Faransa

Yajin aiki ya gurgunta al'amuran yau da kullum a Faransa

Philippe Martinez, Shugaban gamayyar kungiyoyin kwadago a Faransa.
Philippe Martinez, Shugaban gamayyar kungiyoyin kwadago a Faransa. REUTERS / Eric Gaillard

Shugaban gamayyar kungiyoyin kwadago a Faransa Phillipe Martinez, ya sha alwashin ci gaba da jagorantar yajin aiki da ya gurgunta harkokin yau da kullum tsawon sama da makwanni 3, da zummar tilastawa gwamnati janye sauye-sauyen da ta yi kan tsarin biyan kudaden Fansho.

Talla

Yanzu haka dai yajin aikin da aka soma shi ranar 5 ga watan Disambar da muke, ya kafa tarihin zama mafi tsawo a tarihin kasar, tun bayan shekarar 1986 zuwa 1987.

Tattaunawa tsakanin Gwamnati da kungiyoyin kwadago za ta ci gaba ne a ranar 7 ga watan Janairu mai kamawa, bayan yukurin sulhu da aka yi kafin bukukuwan Kirsimeti, tattaunawar da bata yi nasara ba.

Har yanzu dai ana ci gaba da samun tsaiko na zirga-zirga a Faransa, musamman rashin jiragen karkashin kasa da al’ummar kasar suka fi mu’amala da shi, sakamakon yajin aikin ma’aikatar sufuri kan adawa da dokar Fansho.

Zirga-zirgar jiragen kasa na waje da na karkashin kasa dai sun tsaya a birnin Paris da kuma layukan dogo zuwa wasu jihohin kasar a daidai lokacin da ake hutun karshen shekara.

A yayin da kungiyoyin kwadago suka yi shelar gagarumin zanga-zanga ranar 9 ga watan Janairu me zuwa, kamfanin sufurin jiragen kasar Faransa wanda kashi 42 cikin dari da direbobinta na sahun yajin aikin, yace, kashi hamsin na jiragen sa masu tsananin gudu ne kawai zasu yi aiki a birnin Paris da kewaye cikin karshen mako.

Masu yajin aikin dai na adawa ne da shirin gwamnatin shugaban Macron kan dokar biyan kudin Fansho da shekarun ritaya, lamarin da zai kai ga hade wasu kamfanonin Fansho 42 zuwa wuri guda.

Yajin aiki ma’aikatan sufuri mafi tsawo a Faransa shi ne wanda aka yi a shekarun 1986 da kuma 1987, wanda suka dauki tsawon kwanaki 28.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.