Liverpool ta kafa sabon tarihi a gasar Premier

'Yan wasan  Liverpool yayin murnar leshe Supercoupe
'Yan wasan Liverpool yayin murnar leshe Supercoupe AFP/Ozan Kose

Kungiyar Liverpool ta karya duk wasu tarihin sarrafa wasannin bani-in-baka na gasar Premier Ingila, bayan da ta kafa nata tarihin a wasan da ta yi wa Shieffield United raga-raga a daren Alhamis da ci 2 - 0.

Talla

Liverpool da tayi nasara a kussan daukacin wasannin ta na Premier a wannan kakar wasa ta bana, bata nuna alamun gazawa ba na ci gaba da kasancewa a saman teburin gasar.

Nasarar ci 2-0 da ta yi a kan Blades, Liverpool ta ci gaba da kasancewa a matsayi na 13 a teburin Premier, kuma kawom yanzu taci wasanni 19 cikin 20 da ta kara a kakar bana.

Kuma yanzu haka Liverpool ce kungiya ta biyu da ta taba samun maki 58 daga wasanni 20 na farko a gasar Firimiya.

Kwallayen da Mohammed Salah da Sadio Mane suka zura a filin Anfield sun tabbatar da nasarar da suka samu, kuma yin hakan ya nuna cewa sun karya tarihin gasar, a cewar jaridar wasanni ta Daily Star.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.