'Yan sanda sun hallaka wani maharin da wuka a Faransa

'Yan sandan Faransa a Villejuif kusa da birnin Paris
'Yan sandan Faransa a Villejuif kusa da birnin Paris REUTERS

‘Yan sandan Faransa sun harbe wani mutun har lahira bayan da ya daddaba wa mutane wuka a kusa da wani dandalin shakatawa da ke kudancin birnin Paris.

Talla

Yayin farmakin, maharin ya kashe wani mutum guda dake tattaki tare da matarsa, kana ya kuma jikkata wasu mutane biyu, kafin ‘yan sanda su harbe shi.

‘Yan sanda sun bayyana maharin a matsayin matashi mai shekaru 22, to saidai ba’a kai ga gano musabbin aikata hakan ba.

Rohotanni sunce mutun guda ya samu mummunar rauni, yayin da wata mata ta dan ji rauni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.