Turai-Iran

Tarayyar Turai ta bukaci kai zuciya nesa tsakanin Iran da Amurka

Ursula von der Leyen shugabar kungiyar Tarayyar Turai.
Ursula von der Leyen shugabar kungiyar Tarayyar Turai. REUTERS/Vincent Kessler

Kungiyar Tarayyar Turai EU ta bukaci kasashen Iran da Iraqi ka da su fadada rikicin yankin gabas ta tsakiya sakamakon sabuwar takaddamar da ta kunno kai tsakaninsu da Amurka bayan kisan Babban Hafson Sojin Iran da Washington ta yi ta hanyar farmakar Motarshi da jirginta marar matuki a filin jirgin saman Iraqi cikin makon jiya.

Talla

A wata zantawar shugabar kungiyar ta EU Ursula von der Leyen da manema labarai ta bayyana cewa kamata ya yi a warware rikicin ta fuskar Diflomasiyya maimakon daukar matakin Soji.

Kalaman na Ursula na zuwa dai dai lokacin da Iran ta sha alwashin daukar fansa, a bangare guda kuma ake cike da tantama kan yiwuwar kasar ta yi watsi da yarjejeniyar nukiliyar da ta cimma da kasashen duniya.

A cewar von der Leyen maimakon daukar matakan Soji daga bangaren Iran don farantawa Iraqi kamata ya yi a samu fahimtar juna tsakanin kasashen 3.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI