Turai-Majalisar Dinkin Duniya

An samu raguwar masu kaura zuwa Turai- MDD

Wasu 'yan cirani da ke kokarin tsallakawa Nahiyar Turai.
Wasu 'yan cirani da ke kokarin tsallakawa Nahiyar Turai. ELVIS BARUKCIC/AFP

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya kan kaurar baki zuwa nahiyar Turai a shekarar 2019 ya nuna yadda aka samu raguwar adadin bakin hauren da ke tsallakawa nahiyar mafi karanta tun bayan shekarar 2013.

Talla

Sai dai rahoton ya kuma nuna yadda aka samu karuwar ‘yan ciranin da ake tisa keyarsu wajen mayar da su kasashensu a kokarinsu na tsallakawa Turai.

Rahoton ya bayyana cewa duk da yadda ake fuskantar karuwar adadin ‘yan ciranin da ke son tsallaka Turai don samun ingantacciyar rayuwa babu shakka adadin da ke iya sulalewa zuwa kasashen ya ragu wanda rahoton ya alakanta da matakan baya-bayan nan da kungiyar Turai ke dauka.

A cewar rahoton, a yanzu hanyoyin da ‘yanciranin kan yi amfani da su wajen shiga Turai bai wuce ta iyakokin Girka da Bulgaria da kuma Cyprus ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.