Isa ga babban shafi
Faransa

Kungiyoyin kwadago sun ja tunga da gwamnatin Faransa kan fansho

Gangamin mambobin kungiyar kwadago ta CGT a Faransa.
Gangamin mambobin kungiyar kwadago ta CGT a Faransa. AFP Photos/Christophe Simon
Minti 2

Hadakar kungiyoyin kwadago a Faransa, sun sha alwashin ci gaba da yajin aiki baya ga gangamin kalubalantar kudirin gwamnati na gabatar da sabuwar dokar gyara a tsarin fanshon kasar.

Talla

Matakin hadakar kungiyoyin kwadagon na Faransa, na zuwa a dai dai lokacin da shugaba Emmanuel Macron ke shirin gabatarwa majalisar ministocinsa kunshin sabuwar dokar a juma’a mai zuwa, gabanin majalisa ta fara tafka muhawara kansa a ranar 17 ga watan Fabarairu.

Sabon kudirin dokar Fanshon na shugaba Emmanuel Macron ya haddasa kakkarfar zanga-zanga da yajin aikin watanni irinsa na farko a tarihin kasar.

A jawabinsa ta gidan talabijin Philippe Martinez shugaban guda cikin manyan kungiyoyin kwadago a faransar CGT, ya ce za su cigaba da gangami tare da yajin aikin sufuri don kalubalantar kudirin fanshon na Macron wanda karkashinsa ya bukaci kowanne ma’aikaci ya shafe wa’adin shekaru 2 bayan ritaya kafin samun kudaden fansho.

Jagororin masu zanga-zangar dai na samun goyon baya daga bangaren adawa wadanda suma suka kalubalancin sabuwar dokar rityar da ta tsawaita shekarun ajje aiki daga shekara 62 zuwa shekara 64.

A bangare guda sabuwar dokar ta Macron da ke ci gaba da haddasa yamutsi a sassan faransa, na barazana ga rayukan wasu manyan mukarraban gwamnatinsa.

Masu shigar da kara a Faransar sun tabbatar da yadda minstan kudin kasar Bruno Le Maire da minstan kasafi Gerard Darmanin ke fuskantar barazanar kisa daga wasu daidaikun al’ummar kasar dangane da batun sabuwar dokar fanshon ta Macron.

Kafafen yada labaran faransar sun ruwaito yadda guda cikin wasikan da ministocin biyu suka samu, ta bukaci su dakatar da Shugaba Macron daga gabatar da sabuwar dokar kokuma a fuskanci kisan kai marar adadi ga jami’an gwamnati.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.