Turai

Matashi ya kashe mutane shida a Jamus

Yan Sanda  a wani yanki da aka kai hari a Turai
Yan Sanda a wani yanki da aka kai hari a Turai REUTERS/Michele Tantussi

Akalla mutune shida sun rasa rayukansu, sannan da dama suka jikkata sakamakon wani harin bindiga da wani matashi ya kaddamar a kudu maso yammacin kasar Jamus a yau Jumma’a.

Talla

Matashin dan shekara 26 bayan aikata kisan ya kira yan Sanda ,inda ya kuma bayyana cewa shine ya aikata kisan .

Matashin da aka bayyana shi a matsayin wanda ya keda izinin mallakar bindiga.

Tuni aka cafke wani mutun da ke da alaka da maharin kamar yadda majiyar ‘yan sandan kasar Jamus ta bayyana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.