Isa ga babban shafi
Amurka

Lauyoyi sun soma gabatar da hujjojin kare shugaba Trump daga tsigewa

Shugaban masu rinjaye na majalisar datiijan Amurka Mitch McConnell  da Sanata John Cornyn yayin shirin soma sauraron shari'ar tsige shugaba Donald Trump. 16/01/2020.
Shugaban masu rinjaye na majalisar datiijan Amurka Mitch McConnell da Sanata John Cornyn yayin shirin soma sauraron shari'ar tsige shugaba Donald Trump. 16/01/2020. REUTERS/Joshua Roberts/File Photo
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
Minti 2

Lauyoyin fadar White House a karkashin jagoransu Pat Cipollone, sun soma gabatar da hujjojin wanke shugaban Amurka Donald Trump a zauren majalisar dattijai, daga zarge-zargen aikata laifukan da suka bada damar tsige shi.

Talla

Zarge-zargen dai sun hada da neman Ukraine ta yi katsalandan cikin zaben Amurka ta hanyar bata sunan, Joe Biden babban abokin hamayyar Trump, sai kuma hana majalisa gudanar da bincike kan zargin.

Tuni dai majalisar wakilai da ‘yan democrats suka fi rinjaye ta kada kuri’ar tsige shugaba Trump ranar 18 ga Disamban nan daya gabata, inda a yanzu kallo ya koma ga zauren majalisar dattijai mai rinjayen jam’iyyar Republican mai mulki, don ganin yadda makomar shugaban na Amurka za ta kasance.

Tilas dai a samu rinjayen kashi 2 bisa 3 na adadin ‘yan majalisar dattijai kafin tsige shugaba Trump dindindin daga shugabanci, ko kuma ‘yan adadin majalisar dattijan 67 su goyi bayan kudurin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.