Amurka

Trump ya gabatar da shirin sasanta rikicin gabas ta tsakiya

Shugaban Amurka Donald Trump da Fira Ministan Isra'ila Benyamin Netanyahu, yayin gabatar da shirin sasanta rikicin gabas ta tsakiya.
Shugaban Amurka Donald Trump da Fira Ministan Isra'ila Benyamin Netanyahu, yayin gabatar da shirin sasanta rikicin gabas ta tsakiya. REUTERS/Brendan McDermid

Shugaban Amurka Donald Trump ya gabatar da shirin sa na sasanta rikicin Gabas ta Tsakiya wanda ya mallakawa Israila daukacin Birnin Kudus da kuma wasu Yankunan Falasdinawa, yayin da ya bayyana goyan bayan kafa kasar Falasdinu.

Talla

Shi dai wannan shiri mai dauke da shafuka 80 da kuma taswira iyakokin kasashen biyu ya bayyana cewar Israila zata mallake Yankunan Falasdinawa 15 da ta gina gidajen da Yahudawa ke ciki, wadanda akewa lakabi da Yankunan ‘Yan kama wuri zauna.

Tuni wannan shiri wanda ya samu goyan bayan Firaministan Israila Benjamin Netanyahu ya gamu da mummunar suka daga Falasdinawa wadanda suka yi watsi da shi, kuma suka sake jaddada matsayin su na watsi da Amurka a matsayin mai shiga tsakani wajen sasanta rikicin bangarorin biyu.

Shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas ya shaidawa manema labarai cewar babu wani Bafalasdine ko Balarabe da zai amince da wannan shiri, yayin da yace bangarorin Falasdinawa baki daya zasu hada kan su wajen yaki da shi.

Kasar Turkiya ta hanun ma’aikatar harkokin wajen ta ta bayyana shirin a matsayin abinda ba zai yiwu ba, yayin da kungiyar Hamas ita ma tayi watsi da shi.

Ita ma kasar Jordan da aka mallakawa Israila wani yankin kasar ta tace babu wani shirn zaman lafiyar da zai dore muddin ba’a gina shi akan iyakokin shekarar 1967.

Ita kuwa kasar Rasha ta bukaci Israila da Falasdinawa da su zauna teburi guda domin tattaunawa a tsakanin su da zummar kulla yarjejeniya, bayan gabatar da shirin na Amurka, yayin da firaministan Birtaniya Boris Johnson ya bayyana shirin na Trump a mtsayin kyakyawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.