Birtaniya-EU

Birtaniya da EU na ganawar karshe gabanin Brexit

Majalisar Birtaniya.
Majalisar Birtaniya. UK Parliament/Jessica Taylor

Kasashen Turai 27 da suka rage a kungiyar EU na tattaunawar karshe da Birtaniya wadda za ta kammala ficewa daga gungun a gobe Juma’a, inda jumullar kasashen suka rattaba hannu kan yarjejeniyar sabuwar dokar alakarsu da Birtaniyar da za ta fara aiki da sanyin safiyar gobe.

Talla

Yau Alhamis ne dai ke matsayin yini na karshe ga Birtaniya a matsayin mambar kungiyar ta EU, kungiyar da a yanzu za ta kasance mai wakiltar kasashe 27 sabanin 28 da ta ke a baya.

Tun a daren jiya ne Majalisar Turai ta yi zama na musamman inda ‘yan majalisun kasashen 27 suka rattaba hannu kan sabuwar yarjejeniyar alakarsu da Birtaniyar a nan gaba, yarjejeniyar da sanarwar EU ta bayyana cewa za ta fara aiki daga karfe 12 na daren gobe juma’a.

Kawo yanzu dai ana ci gaba da ganawar karshe tsakanin bangarorin biyu, wanda kowanne ke ganin tsaginsa na neman yin raguwar dabara game da rabuwar, yayinda Birtaniyar ta bayyana shirin sakin wata waka ta musamman game da ficewar tun da misalin karfe 11 na daren gobe Juma’a.

Sanarwar da EU ta fitar ta bayyana cewa daga gobe alakarsu da Birtaniya za ta koma tamkar alakarsu da sauran kasashe.

Shekaru 3 kenan ana dambarwa tsakanin Birtaniyar da EU game da shirin Ficewar, matakin da ya sanya murabus din Firaministan kasar biyu wato David Cameron da Theresa May.

A gobe juma’ar ne dai alakar Birtaniyar da EU ta tsawon shekaru 47 za ta kawo karshe ko da dai kasar za ta ci gaba da amfanuwa da tsare-tsare baya ga dokokin kasuwanci dana tafiye-tafiyen tarayyar ta Turai har zuwa karshen shekarar nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.