EU Zata ci gaba da hulda da Birtaniya bayan fitcewa
Wallafawa ranar:
Manyan jami’an Kungiyar Tarayyar Turai sun gana a wannan Juma’ar, inda suka tattauna kan sabon babin da kungiyar za ta bude, yayin da suka gargadi Birtaniya cewa, za ta rasa samun alfanun shakuwar kut-da-kut bayan ficewarta daga nahiyar.
Shugabar Hukumar Kungiyar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta ce, suna son gina kwakkwarar dangartaka tsakaninsu da Birtaniya, amma huldarsu ba za ta kasance tamkar lokacin da kasar ke da matsayin mamba a Turai ba.
Von der Leyen ta ce, dungulewarsu wuri guda, ta kawo musu ci gada a fagen siyasa, yayin da nahiyar ta zamo mai karfi a fannin tattalin arzikin duniya.
A cewar shugabar, kwarewarsu ta nuna musu cewa, babu yadda kungiyar EU za ta karfafa muddin a ka warwatse daga cikinta.
Da misalin karfe 11 na dare agogon birnin Brsussels da London ake sa ran Birtaniya za ta fice daga kungiyar tarayyar Turai, amma za ta ci gaba da kasancewa karkashin dokokin EU ta fannin kasuwanci da tafiye-tafiye a tsawon watanni 11 kafin kasar ta fice baki daya.
A makon gobe ake sa ran Firaministan Birtaniya Boris Johnson ya kaddamar da tsarin cimma yarjejeniyar kasuwanci tsakanin bangarorin biyu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu