Faransa

Mutanen da suka yi damfara da sunan Ministan Faransa

Ministan Harkokin Wajen Faransa  Jean-Yves Le Drian
Ministan Harkokin Wajen Faransa Jean-Yves Le Drian Bertrand GUAY / AFP

Hukumomin Fransa sun gurfanar da wasu mutane da ake zargi da amfani da sunan Ministan Harkokin Wajen kasar, Jean Yves Le Drian wajen damfarar wasu attajirai kudaden da suka kai Euro miliyan 50.

Talla

Biyu daga cikin mutanen na fuskantar tuhumar zamba cikin aminci da sace bayanan Ministan domin amfani da sunansa wajen karbar kudaden da suka zarce Euro miliyan 50 daga attajiran 'yan siyasa da 'yan kasuwa da shugabannin addinai.

Mutanen biyu wadanda 'yan assalin Isra'ila ne mazauna Faransa, sun hada da Gilbert Chikli mai shekaru 54 da Anthony Lasarevitsch mai shekaru 35, yayin da suka jagoranci wasu mutane 5 wajen aikata laifuka, inda wani daga cikin su ke fakewa da sunan Ministan yana waya da mutane.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.