Faransa

Kungiyoyin kwadagon Faransa na shirin sake shiga zanga-zanga nan gaba

Zanga-zangar kungiyoyin kwadago a birnin Marseille na kasar Faransa
Zanga-zangar kungiyoyin kwadago a birnin Marseille na kasar Faransa AFP Photos/Christophe Simon

Kungiyar kwadago ta kasar Faransa a bangaren sufuri a birnin Paris na ta yi kira da a shiga wani sabon yajin aiki daga ranar 17 ga watan Fabarairun wanan wata, ranar da ake sa ran yan Majalisun kasar za su tafka muhawara a majalisar dokokin kasar kan kudirin sake fasalin dokar fansho ta Faransa.

Talla

Faransawa na ci gaba da fuskantar matsalloli biyo bayan kai ruwa rana tsakanin gwamnatin da kungiyoyin kwadagon kasar dangane da dokar fansho.

Wasu alkaluma daga kungiyoyin kwadagon kasar na nuna ta yadda al’amura suka tsaya cik a bangaren sufuri a birnin Paris har na tsawon makonni 6 daga farkon watan Disamba har zuwa tsakiyar Janairu sakamakon yajin aikin da kungiyoyin kwadago suka shiga don nnuna adawa da aniyar gwamnatin kasar na yiwa wa dokar fansho garambawul, lamarin da kungiyoyin kwadagon kasar suka ce babu adalci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.