Faransa

An gano wasu yan Birtaniya dauke da Coronavirus a Faransa

Wasu daga cikin mutanen dake dauke da cuitar Coronavirus  a Faransa
Wasu daga cikin mutanen dake dauke da cuitar Coronavirus a Faransa JEFF PACHOUD / AFP

Hukumomin Faransa sun ce wasu yan kasar Birtaniya guda biyar sun kamu da cutar Coronavirus cikin su harda karamin yaro. Firaminista  Edoaurd Philippe ya kira taron ministocin kasar don tattaunawa a kai.

Talla

Ministar lafiya ta kasar Faransa Agnes Buzyn ce ta sanar da haka,inda tace yanzu haka an gano mutane 11 dake dauke da cutar,wandada suka hada da wani dan Birtaniya da ya dawo daga Singapore.

Sai dai Ministar tace ya zuwa yanzu babu daya daga cikin su da ya nuna alamar fuskantar mawuyacin hali,yayin da shi kuma dan Birtaniya da ya dauko cutar daga Singapore ya koma gida.

Ministar ta ce hukumomin Faransa da Singapore na hada kai wajen gano mutanen da suka yi mu'amula da mutumin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.