Sauyin yanayi

Guguwar Ciara ta hana hada-hada a Turai

Yanayin guguwar Ciara da ta afka wa wani yanki na Turai
Yanayin guguwar Ciara da ta afka wa wani yanki na Turai GLYN KIRK / AFP

Wata mahaukaciyar guguwa mai dauke da ruwan sama da aka yi wa lakabi da Ciara ta afka wa wani yanki na kasashen Turai, abin da ya tilasta soke sauka da tashin daruruwan jiragen sama da zirga-zirgar jiragen kasa, yayin da daruruwan gidaje suka rasa wutar lantarki a Birtaniya da Ireland.

Talla

Guguwar ta kuma tilasta soke wasanni da tafiye-tafiye a yankin arewacin nahiyar Turai.

A Birtaniya rahotanni sun ce, guguwar mai tsala gudun kilomita 140 a sa’a guda ta katse wa gidaje sama da dubu 30 hasken lantarki a gabashin birnin London, yayin da ta katse wa wasu gidajen dubu 14 lantarkin a Ireland.

Karin kasashen da aka yi hasashen guguwar ta Ciara za ta afka wa sun hada da Faransa da Belgium da Netherlands da Switzerland da kuma Jamus.

A Jamus din, tuni aka dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa masu cin dogon-zango a mafi akasarin arewa maso yammacin kasar saboda guguwar ta Ciara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.