Turai

Macron ya zargi Rasha da yunkurin wargaza dimokaradiyar Turai

Shugaban Faransa Emmanuel Macron.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron. REUTERS/Andreas Gebert

Shugaban Faransa Emmanuel Macron, ya gargadi kasashen Turai da cewar, Rasha za ta ci gaba da kokarin wargaza dimokaradiyyar kasashen, ta hanyoyin yin kutse ko katsalandan a zabukansu, da kuma kai musu hare-hare ta hanyar kutsen satar bayanai ta shafukan Intanet.

Talla

Shugaba Macron ya bayyana haka ne, yayin jawabi a zauren taron Yayin taron kasa da kasa kan tsaron duniya dake gudana a birnin Munich na Jamus.

Shugaban na Faransa ya ce, Rasha za ta yi kokarin cimma burikanta ne ta hanyar amfani da sojojin haya, da kuma kwarrarun jami’anta na liken asiri.

Sai dai shugaban ya ce bayaga Rasha, Amurka ma na da burin yin katsalandan a zabukan Turai, dan haka akwai bukatar hada giwa don fuskantar barazanar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.