Turai ta yi tir da matakin Amurka kan takaita ayyukan sojinta

Shugaban Faransa a taron birnin Munich na kasar Jamus
Shugaban Faransa a taron birnin Munich na kasar Jamus CHRISTOF STACHE / AFP

Cacar Baka ta barke tsakanin Amurka da kasashen Turai kan zargin dakushewar kimar nahiyar Turai da kuma janyewar Amurka daga fagen siyasar duniya a wajen taron duniya kan harkokin tsaron dake gudana a Munich dake kasar Jamus.

Talla

Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya yi watsi da zargin da shugabannin Turai ke yi cewar Amurka na janyewa daga fagen duniya wajen janye dakarun ta daga wasu kasashen duniya da kuma rage karfin fada aji a kungiyar kawancen tsaro ta NATO.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron wanda ke jagorancin wani sabon yunkuri na ganin kasashen Turai sun daina dogaro da Amurka wajen kafa runduna mai karfi da zata dinga samar musu da tsaro, yace ba zasu nade hannu suna sanyawa Amurka ido tana kare su ba.

Pompeo yace rahotannin da ake bayarwa game da rugurgujewar hadin kai tsakanin kasashen kungiyar NATO sun wuce makadi da rawa, domin abinda Amurka kawai ke bukata shine kowacce kasa ta dinga bada kudaden da aka sanya mata maimakon dogara da Amurka kacaukan.

Shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeir ya zargi Amurka ta bijirewa kasashen duniya wajen yin gaban kan ta na daukar matakin dake illa ga makotan ta da kuma kawayen ta.

Shugaba Macron wanda ya goyi bayan matsayin Jamus, yace yayin da Amurka ke sake tunani kan dangantakar ta da kasashen Turai, ya zama wajibi a gare su da hada kan su wajen fuskantar kalubalen dake gaban su.

Macron yace ya zama wajibi su sake fasalin dangantakar su wadda zata basu damar dogaro da kai da kuma karfin fada aji a siyasar duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.