Turai-Birtaniya

Birtaniya za ta fuskanci tattaunawa mai tsauri kan kasuwanci - Faransa

Ministan Harkokin Wajen Faransa  Jean-Yves Le Drian.
Ministan Harkokin Wajen Faransa Jean-Yves Le Drian. Bertrand GUAY / AFP

Faransa ta gargadi Biritaniya da cewar za ta fuskanci tattaunawa mai tsauri dangane da sabuwar yarjejeniyar kasuwancin da za ta kulla da kungiyar Tarayyar Turai EU, da ta fice daga cikinta.

Talla

Ministan Harkokin Wajen Faransa Jean-Yves le Drian ne ya bayyana hakan a taron harkokin tsaron duniya da ya gudana a birnin Munich na kasar Jamus.

Duk da cewa sai a watan gobe za a soma tattaunawa kan yarjejeniyar hulda da juna tsakanin EU da Burtaniya, akwai sabani tsakanin bangarorin 2 kan ka’idojin shigar kamfanonin kudin Burtaniya cikin kasashen Turai bayan rabuwarsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.