Faransa

Majalisar Faransa ta soma mahawara kan dokar fansho

Zauren majalisar dokokin Faransa.
Zauren majalisar dokokin Faransa. REUTERS/Benoit Tessier

Majalisar dokokin Faransa ta fara tafka mahawara kan dokar Fansho, dake haifar da tada jijiyoyin wuya tsakanin gwamnati, ‘yan adawa da kuma kungiyoyin kwadago a kasar.

Talla

adawar dai sun bayyana cewa a shirye suke su haifar da tarnaki ga shirin dokar da aka kwashe shekaru 2 ana kai ruwa rana a kansa.

An dai shafe tsawon shekaru 2 ana tafka zazzafar mahawara kan shirin dokar harajin a Majalisar dokokin Faransa, abinda ya kai ga yaje yajen aiki, da kuma jerin zanga-zanga mafi muni a tarihin kasar, sai dai duk da haka gwamnatin shugaba Emanuel Macron ta janye aniyar soma aiwatar da dokar.

Sashin dokar fanshon da ya fusata kungiyoyin kwadagon Faransa dai shi ne karin shekarun ritaya daga 62 zuwa 64 da kuma banbanta adadin kudaden da za a biya wadanda suka zabi ajiye aiki a shekarun.

Baya ga karin shekarun ritaya, daya daga cikin sauye-sauyen da shugaba Emmanuel Macron ke son yi shi ne hade kamfanonin lura da hakkokin ‘yan fansho 42 zuwa kamfani 1.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI