Birtaniya-Turai

Shirin Birtaniya kan shige da fice ya gamu da kakkausar suka

Firaministan Birtaniya Boris Johnson.
Firaministan Birtaniya Boris Johnson. Augstein/Pool via REUTERS

Gwamnatin Birtaniya na fuskantar kakkausar suka game da sabon shirin da take yi kan shige da fice, wanda ta tsara shi ta inda za ta maye gurbin ma’aikatan da ke samar da ayyukan yi masu araha da kwararrun ma’aikata da ke amfani da harshen Ingilishi.

Talla

Ana sa ran gwamnatin Birtaniyar ta fara aiwatar da sauye - sauyen ne a ranar daya ga watan Janairun 2021, daga nan ne ma za ta karbe ragamar tafiyar da kan iyakokinta kacokan, wadda hakan shi ne babban burin masu adawa da ci gaba da kasancewa tare da Tarayyar Turai.

Ministan cikin gida Priti Patel ya bayyana matakin a matsayin mai tsauri kuma mai cike da fa’ida, yana mai cewa zai bai wa bakin haure, kwararru damar samun biza cikin sauki, sannan kuma akasin haka ga wadanda ba kwararru ba.

Wadannan sauye-sauye su ne mafi girma a manufofin bakin haure na kasar a cikin shekaru 50 da suka gabata, kuma za a gabatar da su gaban majalisar dokoki, inda Firaminista Boris Johnson ke da gagarumin rinjaye.

Sai dai an caccaki gwamnatin na jam’iyyar Conservative da gaza yin nazari kan tasirin sauye-sauyen nata a kan tattalin arziki, yayin da kasancewa masu masana’antu na dogara ne ga bakin haure ke diga ayar tambaya ga nasarar shirin.

A waje daya kuma, Tarayyar Turai ta ce ta fahimci yadda Birtaniya ke daukin tafiyar da kan iyakokinta, sai dai ta yi kashedin cewa tattaunawa tsakaninta da Birtaniya game da yadda dangantaka zata kasance tsakaninsu nan gaba za ta yi tsauri.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.