London

An kai harin wuka a Masallacin London

Wasu daga cikin jami'an 'yan sandan birnin London
Wasu daga cikin jami'an 'yan sandan birnin London REUTERS/Toby Melville

An cafke wani mutum bisa zargin sa da yunkurin kisa bayan ya kaddamar da harin wuka a cikin wani Masallaci da ke tsakiyar birnin London.

Talla

Maharin ya jikkata wani dattijo da ya haura shekaru 70, yayin da jami’an agajin gaggawa suka halarci babban Masallacin da ke Park Road don agazawa.

Tuni aka garzaya da mutumin zuwa asibiti kuma an tabbatar cewa, ba ya cikin mummunan hali.

Jami’an ‘yan sanda sun ce, ba a kallon wannan harin a matsayin na ta’addanci

Sanarwar da Masallacin ya fitar, ta ce, mutumin da aka jikkata shi ne ladanin Masallacin, kuma an daba masa wuka ne a lokacin sallar La’asar.

Masallata ne suka tsare maharin kafin jami’an ‘yan sanda su hallara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.