Birtaniya za ta fara bayar da Fasfo na kashin kanta

Firaministan Birtaniya Boris Johnson.
Firaministan Birtaniya Boris Johnson. Augstein/Pool via REUTERS

Ma’aikatar harkokin wajen Birtaniya ta sanar da shirin fara bayar da shudin Fasfo a farkon wata mai kamawa, wanda ke zuwa a karon farko tun bayan fasfon hadaka na shekarar 1988 da kasar ta fara bayarwa karkashin tsarin kungiyar Tarayyar Turai.

Talla

Matakin wanda ke zuwa bayan nasarar Birtaniyar ta kammala ficewa daga EU, A cewar ministan harkokin cikin gida Priti Patel yanzu Birtaniya za ta fara bayar da Fasfo makale da tambarin kasar, kuma wanda za ta rika sarrafawa a cikin gidanta.

Tsohon Fasson hadaka da Birtaniya ke amfani da shi kafin ficewa daga EU, Poland ce ke samar da shi gabanin damkawa Faransa ragamar ci gaba da samarwa a shekarun baya-bayan nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.