Faransa

Faransa ta kwance guda cikin Tashoshinta na Nukiliya

Guda cikin tashoshin nukiliyar Faransa.
Guda cikin tashoshin nukiliyar Faransa. AFP/Guillaume Souvant

Gwamnatin Faransa ta fara aikin kwance tashar nukiliyarta mai samar da lantarki mafi dadewa ta EDF, matakin da ke zuwa karkashin shirinta na rage amfani da nukiliya ko da dai shirin bazai shafi bangaren nukiliyar sarrafa makmai ba.

Talla

Nukiliyar wadda ta shafe shekaru 43 tana aikin samar da lantarki a Faransar aikin kwance na zuwa duk da korafe-korafen kungiyoyin kwadago har ma zanga-zangar wasunsu kan yadda matakin zai haifar da tarin marasa aikin yi, ko da masu fafautukar yaki da amfani da nukiliya na ganin kwamnatin na kan daidai.

Bayan aikin kwance tashar nukiliyar ta EDF da ke Fassenheim a yankin Rhine da ke gabashin Faransar gab da iyakarta da Jamus, a ranar 30 ga watan Yuni mai zuwa ne kuma za a sake kulle tsahar nukiliyar ta biyu kamar yadda gwamnati ta alkawarta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.