Faransa-Birtaniya

Macron ya nuna damuwa kan yarjejeniyar kasuwancin EU da Birtaniya

Shugaban Faransa Emmanuel Macron.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron. Jean-Francois Badias/Pool via REUTERS

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce bashi da tabbaci amma, abu ne mai yiwuwa yarjejeniyar kasuwanci ta kammala kulluwa tsakanin kungiyar tarayyar Turai da Birtaniya kafin karshen shekarar nan.

Talla

Birtaniyar dai na da damar kammala kulla yarjejeniyar kasuwanci cikin sauki, tsakaninta da kungiyar gungun kasashen na Turai 28 kafin nan da watan Disamba.

Sai dai shugaba Emmanuel Macron ya bayyana cewa ba abu ne mai sauki iya kammala kulla yarjejeniyar cikin watanni 9 da suka ragewa Birtaniyar ba.

A wata ganawar Macron da kungiyar Masuntan Faransa yayin wani bikin amfanun gona a Paris, ya ce matakan da Birtaniya ke dauka game da kasuwanci na nuna cewa za a kai ruwa rana kafin iya kulla yarjejeniyar.

Masunta Faransa wadanda kai tsaye ficewar Birtaniya ya shafi kashi 90 na ayyukansu na fatan kammala kulluwar yarjejeniyar kasuwancin don dorewar kasuwanci wanda ya fin kankama a iyakar ruwan Faransa da Birtaniya.

A ranar 31 ga watan Janairu ne Birtaniyar ta kawo karshen zamanta na shekaru 47 a cikin kungiyar ta EU matakin da ke zuwa bayan zaben raba gardamar ficewa a 2016 da ya nuna fiye da rabin al’ummar kasar sun goyi bayan ficewa.

Faransa da sauran kasashen Turai dai na son ci gaba da samun damar kamun kifi a gabar ruwan na Birtaniya, sai dai karkashin yarjejeniyar ficewar kasar daga EU ta bukaci cikakken iko da ilahirin gabar ruwanta koda dai sabuwar yarjejeniyar kasuwanci tsakaninta da kungiyar ka iya yin sassauci kan batun.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.