Faransa-Girka

Faransa da Girka za su sanya hannu kan yarjejeniyar tsaro

Ministan tsaron Faransa Florence Parly tare da sojojin kasar
Ministan tsaron Faransa Florence Parly tare da sojojin kasar Daphné BENOIT / AFP

A cikin watanni masu zuwa ne Girka za ta sanya hannu a yarjeniyoyi kan tsaro da Faransa, kamar yadda ministocin tsaron kasashen biyu suka sanar, watanni bayan irin wannan yarjeniyoyin tsakanin Girka da Amurka.

Talla

Ministar Tsaron Faransa Florence Parly ta shaida wa manema labarai cewa kasashen biyu sun kudiri aniyar karfafa dangantaka ta fannin tsaro jim kadan bayan tattaunawarta da takwaranta  Nikos Panagiotopoulos a birnin Athens.

Daga cikin yarjeniyoyin da za a sanya hannu a kai a watan Yuni mai zuwa har da ta atisayen hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu, da kuma ta kara yawan sojojin ruwan su a gabashin yankin tekun Mediterranean.

Ministar tsaron Faransa, Parly ta kuma ce jiragen yakin kasar samfurin Rafale za su shiga atisayen soji da Girka ke yi duk shekara, wadda aka wa lakabi da Iniochos, a watan Mayu.

Girka ta kagara ta samu goyon bayan abokan huldar kungiyar Tarayyar Turai da na kungiyar tsaro ta NATO, musamman a wannan lokaci da zaman tankiya ke tsananta tsakaninta da makwafciyarta Turkiya, biyo bayan takaddama kan makamashi da bakin haure.

Kuma duk da yanayi na kamfar kudi da ta tsinci kanta a sakamakon bashi da ya yi mata kanta, gwamnatin Girka ta bayyana aniyar sayo makamai daga Amurka da Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.