Faransa

kotun Faransa ta daure matashin da ya je Syria yaki shekaru 12

Tutar Faransa
Tutar Faransa RFI

WATA Kotu a Faransa ta yanke hukuncin daurin shekaru 12 akan wani matashi mai suna Reda Hame saboda samun sa da laifin tafiya kasar Syria domin shiga yaki, bayan ya samu horo daga hannun mutumin da ya kitsa harin da aka kai Paris a shekarar 2015.

Talla

Rahotanni sun ce Abdelhamid Abaaoud wanda ya kitsa harin da ya hallaka mutane 130 a Paris ya koyawa Hame yadda ake sarrafa makamai da gurneti, kafin daga bisani ya kai shi iyakar Turkiya domin kai hari a madadin kungiyar IS.

An dai kama Hame ne bayan ya koma Faransa, inda ya bayyana nadamar sa da halin da ya samu kan sa.

Daruruwan matasa daga Faransa suka tafi Syria domin shiga yaki a karkashin kungiyar IS, yayin da aka daure da dama daga cikin wadanda suka koma gida.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.