corona - Italy - Iran

Minista ya kamu da cutar Coronavirus a Iran

Wasu Iraniyawa a birnin Tehran sanye da mayanin fuska don kariya daga cutar coronavirus
Wasu Iraniyawa a birnin Tehran sanye da mayanin fuska don kariya daga cutar coronavirus ATTA KENARE / AFP

Yayin da annobar coronavirus ke ci gaba da tada hankulan al’umma a sassan duniya, inda har ministocin lafiya na kasashen Turai ke taru a Rome, yanzu haka ma’aikatar lafiya ta Iran ta sanar cewa mataimakin ministanta ya kamu da cutar.

Talla

A Italiya, inda ministocin lafiya na kasashen Turai ke taro don nemo hanyar dakile cutar ta coronavirus, hukumomi a wasu jihohi biyu na kasar, wato Tuscany da Sicily sun sanar da bullar cutar.

A wannan Talatar a Iran, ma’aikatar lafiya ta sanar da cewa mataimakin ministanta Iraj Harirci, wanda ke kan gaba wajen kokarin yakar wannan cuta, tun da ta bulla a kasar ya harbu da cutar, bayan ta ce adadin wadanda cutar ta kashe ya kai 15, sannan mutane 34 sun kamu a baya bayan nan.

Hukumomi a Turkiyya sun bayyana killace fiye da ‘yan kasar 100 da suka dawo daga Iran, tare da bayyana aniyar garkame iyakokinta da Iran.

Ya zuwa yanzu Turikiyya ba ta sanar da bullar cutar a kasar ba, yayin da Croatia ta tabbatar da cewa wani mutum da ya dawo kwanan nan daga Italiya ya kamu da cutar.

A cewar Hukumar Lafiya ta Duniya, mutane 2600 sun mutu a China, kuma sama da dubu 77 ne suka harbu, yayin da a wajen China cutar ta kama mutane 2700, tare da kashe 40.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.