Faransa

An fara shari’a tsohon Firaministan Faransa Francois Fillon

Tsohon Franministan Faransa François Fillon ya isa kotu inda ake tuhumar sa da almundahana da dukiyar kasar.
Tsohon Franministan Faransa François Fillon ya isa kotu inda ake tuhumar sa da almundahana da dukiyar kasar. STEPHANE DE SAKUTIN / AFP

Kotu a Faransa ta fara sauraron tuhumar da ake yiwa tsohon Firaminista Francois Fillon da uwargidan sa Penelope na karkata akalar kudaden hukuma wajen zambatar gwamnatin.

Talla

Masu gabatar da kara sun ce Fillon ya sanya sunan matar sa cikin ma’aikatan dake taimaka masa a Majalisa tsakanin shekarar 1998 zuwa 2013, inda aka dinga biyan ta euro 10,000 kowanne wata ba tare da tayi aikin komai ba.

Idan kotu ta tabbatar da wannan zargi, ana iya daure Fillon da uwargidan sa shekaru 10 a gidan yari da kuma tara mai karfi.

Wannan zargi na almundahana na daga cikin abinda ya hana Fillon samun nasara a zaben shekarar 2017 duk da farin jinin da yake da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.