Faransa

Faransa ta hana taron jama’ar da ya wuce mutane 5,000

Taron majalisar ministocin Faransa dangane da batun Coronavirus
Taron majalisar ministocin Faransa dangane da batun Coronavirus Jean-Claude Coutausse/Pool via REUTERS

Gwamnatin kasar Faransa ta bayyana shirin hana duk wani taron da ya kunshi mutane sama da 5,000 da za’a gudanar da shi a cikin daki saboda kaucewa yaduwar cutar coronavirus.

Talla

Ministar lafiya Olivier Veran tace matakin ya biyo bayan taro na musamman da suka yi kan barazanar cutar, wadda yanzu haka ta kama mutane 73 a cikin kasar.

Saboda daukar wannan mataki, an soke shirin tseren yada kanin wani da aka shirya yi gobe a birnin Paris tare da bikin baje kolin kayan amfanin gona.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron yace gwamnatinsa na cikin shirin ko ta kwana, don tunkarar annobar murar mashako ta Coronavirus da yace kasar na fuskanta, bayan da kididdiga ta nuna karuwar wadanda suka kamu da ita a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.